Matthew 8

Mutum Mai Kuturta

1Da ya sauko daga gefen dutsen, sai taron mutane mai yawan gaske suka bi shi. 2Wani mutum mai kuturta ya zo ya durƙusa a gabansa ya ce, “Ubangiji, in kana so, kana iya tsabtace ni.”

3Yesu ya miƙa hannunsa ya taɓa mutumin. Ya ce, “Ina so, ka tsabtace!” Nan da nan aka warkar
Girik aka tsabtace
da shi daga kuturtarsa.
4Sai Yesu ya ce masa, “Ka lura kada ka gaya wa kowa. Sai dai ka tafi, ka nuna kanka ga firist ka kuma yi bayarwar da Musa ya umarta, a matsayin shaida gare su.”

Bangaskiyar Jarumi

5Da Yesu ya shiga Kafarnahum, sai wani jarumi ya zo wurinsa, yana neman taimako. 6Ya ce, “Ubangiji, bawana yana kwance a gida shanyayye, yana kuma shan azaba ƙwarai.”

7Yesu ya ce masa, “Zan je in warkar da shi.”

8Jarumin ya amsa, “Ubangiji, ban cancanci in sa ka zo gidana ba, ka dai yi magana kawai, bawana zai warke. 9Gama ni kaina mutum ne a ƙarƙashin iko, da kuma sojoji a ƙarƙashina. Nakan ce wa wannan, ‘Je ka,’ sai yǎ tafi; wancan kuma, ‘Zo nan,’ sai yǎ zo. Nakan ce wa bawana, ‘Yi wannan,’ sai kuwa yǎ yi.”

10Da Yesu ya ji wannan, sai ya yi mamaki ya kuma ce wa waɗanda suke binsa, “Gaskiya nake gaya muku, ban taɓa samun wani a Israʼila da bangaskiya mai girma haka ba. 11Ina kuma gaya muku da yawa za su zo daga gabas da kuma yamma, su ɗauki wuraren zamansu a biki tare da Ibrahim, Ishaku, da Yaƙub a cikin mulkin sama. 12Amma za a jefar da ʼyaʼyan mulki waje, zuwa cikin baƙin duhu, inda za a yi kuka da cizon haƙora.”

13Saʼan nan Yesu ya ce wa jarumin, “Je ka! Za a yi bisa ga bangaskiyarka.” A daidai wannan lokaci bawansa kuwa ya warke.

Yesu Ya Warkar da Mutane da Yawa

14Da Yesu ya zo cikin gidan Bitrus, sai ya ga surukar Bitrus tana kwance a gado tana da zazzaɓi. 15Ya taɓa hannunta sai zazzaɓin ya sake ta, ta kuwa tashi ta fara yin masa hidima.

16Da yamma ta yi, aka kawo masa masu aljanu da yawa, ya kuwa fitar da ruhohin ta wurin magana, ya kuma warkar da dukan marasa lafiya. 17Wannan ya faru ne domin a cika abin da aka faɗa ta bakin annabi Ishaya cewa:

“Ya ɗebi rashin lafiyarmu,
ya kuma ɗauki cututtukarmu.”
Ish 53.4

Wahalar Bin Yesu

18Da Yesu ya ga taron mutane kewaye da shi, sai ya ba da umarni a ƙetare zuwa ɗayan hayin tafkin. 19Sai wani malamin dokoki ya zo wurinsa ya ce, “Malam, zan bi ka duk inda za ka.”

20Sai Yesu ya amsa, ya ce, “Yanyawa suna da ramummuka, tsuntsayen sararin sama kuma suna da sheƙuna, amma Ɗan Mutum ba shi da wurin da zai sa kansa.”

21Sai wani almajiri ya ce masa, “Ubangiji, da farko bari in je in binne mahaifina.”

22Amma Yesu ya ce masa, “Ka bi ni, ka bar matattu su binne matattunsu.”

Yesu Ya Kwantar da Hadari

23Sai ya shiga jirgin ruwa, almajiransa kuwa suka bi shi. 24Ba zato ba tsammani, sai wani babban hadari ya taso a tafkin, har raƙuman ruwan suka sha kan jirgin. Amma Yesu yana barci. 25Almajiran suka je suka tashe shi, suna cewa, “Ubangiji, ka cece mu! Za mu nutse!”

26Ya amsa ya ce, “Ku masu ƙarancin bangaskiya, me ya sa kuke tsoro haka?” Saʼan nan ya tashi ya tsauta wa iskar da kuma raƙuman ruwan, sai wuri ya yi tsit gaba ɗaya.

27Mutanen suka yi mamaki suka ce, “Wane irin mutum ne wannan? Har iska da raƙuman ruwa suna masa biyayya!”

Warkar da Mutum Biyu Masu Aljanu

28Da ya isa ɗayan gefen a yankin Gadarenawa
Waɗansu rubuce rubucen hannu na dā suna da Gergesenawa; waɗansu kuma Gerasenawa ne a nan
(ko kuwa Gerasenawa), sai ga mutum biyu masu aljanu suna fitowa daga kaburbura suka tarye shi. Su abin tsoro ne ƙwarai, har ba mai iya bin wannan hanya.
29Suka yi ihu suka ce, “Me ya haɗa ka da mu, Ɗan Allah?” Ka zo ne nan don ka ji mana kafin lokaci yǎ yi?

30Nesa kaɗan da su kuwa akwai babban garken aladu da yake kiwo. 31Aljanun suka roƙi Yesu suka ce, “In ka fitar da mu, tura mu cikin garken aladun nan.”

32Ya ce musu, “Ku tafi!” Sai suka fita suka shiga cikin aladun, dukan garken kuwa ya gangara a guje daga kan tudun zuwa cikin tafkin aladun kuma suka mutu a cikin ruwa. 33Masu kiwon aladun suka ruga, suka je cikin gari suka ba da labarin dukan wannan, haɗe da abin da ya faru da mutanen nan masu aljanu. 34Sai dukan garin suka fito don su taryi Yesu. Da suka kuwa gan shi, sai suka roƙe shi yǎ bar musu yanki.

Copyright information for HauSRK